TSARO: ATIKU NA GOYON BAYAN MAJALISA KAN BATUN 'YANSANDAN JIHOHI
- Wasu na ganin idan jihohi na da 'yansandansu za'a sami
tsaro
- Wasu kuma na ganin gwamnoni zasu yi karfi sosai
- Atiku na bayan majalisa kan batun a baiwa jihohi dama a
doka
Matsalar tsaro ta addabi jihohin kasar nan, inda ko wanne
yanki yake fama da nasa, daga rikicin manoma-makiyaya, sai na kabilanci, sai na
addinanci, da ma na siyasa, sai kuma na 'yan daba, da ma na 'yan fashi da masu
garkuwa da mutane. A kuma bangare daya, akwai matsalar ta'addanci, inda Boko
Haram ke kan ganiyar durkusar da kasar baki daya. Kokarin dawo da zaman lafiya
ya sanya wasu ke ganin tunda gwamnatin Najeriya ta kasa, a baiwa jihohi damar
su tsare jama'arsu da kansu.
Bayan da shuwagabannin majalisa suka nuna suna goyon bayan
hakan, yanzu shima tsohon mataimakin shugaba Obasanjo, Atiku Abubakar, yace, ya
dawo daga rakiyar gwamnatin tarayya, domin ta gaza tsare jama'a, don haka, a
baiwa gwamnoni damar daukan jami'an tsaron jama'arsu a hukumance.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku