SOJIN SAMAN NAJERIYA SUN YI WA 'YAN BOKO HARAM RAGA-RAGA DA JIRAGEN YAKI


Dakarun sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force (NAF) ta ce rundunar ta ta shirin ko ta kwana ta musamman dake a karkashin babbar rundunar Operation Lafiya Dole sun yi nasarar yin raga-raga da 'yan ta'addan Boko Haram a kauyukan Bulagalaye da kuma Kwakwa, dukan su a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, AVM Olatokunbo Adesanya shine ya sanarwa da manema labarai hakan a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Abuja.
A wani labarin kuma, Rundunar sojin saman Najeriya Nigerian Air Force (NAF) a ranar Alhamis din da ta gabata ta kara yaye matukan jiragen yaki a makarantar koyon tukin jiragen dake a garin Kainji. Da yake jawabi a wajen yaye daliban, Hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar da shugaban makarantar Air Vice Marshal Mohammed Idris ya wakilta ya bayyana yaye daliban a matsayin babban cigaba a kasar musamman ma wajen yaki da take yi da 'yan ta'adda

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments