SIYASA: 'YA KU 'YAN NAJERIYA, BA LALLAI FA AYI ZABEN 2019 BA'

- Uche Secundus yace bai yarda kacokan za'a yi zaben badi ba
- Hukumar zabe ta fidda jaddawalin zaben tun bara.



A ziyararda ciyamomin kananan hukumomi suka kai sakatariyar PDP, Uche Secondus, dan karadin PDP, yace ba fa lallai ayi ma zaben badi ba, domin shi bayyi amanna da yadda ake shirin yin zaben ba. A cewarsa, muddin zabukan mako mai zuwa na Ekiti basu tafi yadda aka tsara ba, kuma ba'a yi adalci a zaben ba, akwai alammar na badi ma na kasa gaba-daya baza ayi adalcin ba, don haka ya gargadi APC da kada ta kuskura ta murde zaben Ekiti.
A yanzu dai, akwai jaddawalin zabukan s=kasar nan na shekaru kusan 30 INEC hukumar zabe ta rattaba ta ajiye, wanda take sa rai za'a bi sau da kafa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments