RUWA YA CI RAN ‘YAN MATA HUDU A HADARIN KWALE-KWALE A KATSINA
Rundunar
‘Yan sandan jihar Katsina ta bayyyana mutuwar wsu ‘yan mata hudu sanadiyyar
hadarin kwale-kwale a Madatsar Ruwan Mashigi, cikin Karamar Hukumar Kankara.
Kakakin
jami’an tsaron Gambo Isah ne ya ce hadarin ya afku ranar Lahadi da rana tsaka.
Ya
kara cewa dukkan mamatan ‘yan kauyen Danzango ne, sun shiga kwale-kwalen da
niyya a tallaka da su tsallaken dam su sayo kayan masarufi a lokacin da
kwale-kwalen ya tuntsire da su.
Isah
ya bayyana sunayen mamatan da Yasira Suleiman, Shafawu Saidu, Firdausi Ibrahim
da kuma Rakiya Isa, dukkan su ‘yan shekara 16 da haihuwa.
Wasu
mutane biyu da aka ceto a cikin ruwan, an garzaya da su asibitin Kankara domin
a yi musu kulawar gaggawa.
Ya
de Maryam Zubairu mai shekaru 13 da matukin jirgin, Abdullahi Muntari ne suka
tsira.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku