RAHOTON UNICEF TA NUNA CEWA YARA MILIYAN 123 NE AKA YI WA RIGAKAFI A DUNIYA A SHEKARAR 2017
Majalisar dinkin duniya (UN) ta
bayyana cewa sun sami nasarar yi wa yara miliyan 123 allurar rigakafin cutar
tsatasa wato ‘Tetanus’ a duniya cikin shekarar 2017.

Majalisar ta fadi haka ne bisa ga
sakamakon rahotannin da WHO da UNICEF suka mika mata.
Majalisar
ta ce duk da wannan nasarori da suke samu daga wannan bincike ya nuna cewa
akwai yara miliyan 20 a duniya da basu sami yin rigakafi ba.
Bayan
haka kuma an gano cewa akwai jarirai sama da miliyan 4 da aka yi musu allurar
rigakafi a 2017, da hakan ya nuna an sami kari kan yawan wadanda aka yi wa a
2010.
Rahoton
ya nuna cewa kasahe 167 sun hada har da maganin bakon dauro, sannan kuma 162 na
amfani da maganin rigakafi na rubella ga jariran da hakan ya sa a ka sami
karuwa daga kashi 35 bisa 100 zuwa kashi 52 na wadanda aka yi wa rigakafin.
Wasu
daga cikin dalilan da ya sa aka yi ta samun matsaloli wajen yi wa yara allurar
rigakafi sun hada da yake-yake da ake fama dasu a kasashen duniya da kuma kuma
karyewar tattalin arzikin wasu kasashe musamman masu tasowa da matsanancin
talauci.
Bayan
haka UN ta ce ta sami maganin rigakafin cututtukan sankara dake kama mahaifa,
zazzabin cizon sauro, sankarau da Ebola.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku