YAN BINDIGA SUN FAR MA KAUYEN MALIKAWA A JIHAR ZAMFARA


Rahoton da muke smau yanzun nan na nuna cewa yan bindiga sun kai farmaki kauyen Malikawa a Gidan Gog, karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
A lokacin da muka samu wannan rahoto, yan bindigan suna kan kashe mutane yayinda suka shiga kauyen suna harbin kan mai uwa da wabi. Kungiyar Amnesty International ta bayyana hakan a shafin sada zumuntar cewa: "Ana kan kai hari yanzu a Malikawa da ke Gidan Goga, karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara. Yan bindiga sun shiga kauyen suna harbi." A watan Mayu, yan bindigan sun hallaka akalla mutane 30 a kauyen Malikawan da wannan abu ke faruwa yau. Tun lokacin, mutan kauyen sun kasance cikin fargaba. Za mu kawo muku cikakken rahoton..

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com 

Comments