R-APC ZATA IYA TSAYAR DA DAN TAKARAR SHUGABAN KASA - BUBA GALADIMA


Sabuwar jam'iyyar APC wanda akafi sani da R-APC, tace a shirya take ta fitar da dan takarar shugabancin kasa a zaben 2019.



Buba Galadima, wanda shine jagoran r-APC, ne ya bayyana cewa sabuwar APc zata fitar da dan takarar shugabancin kasar ta muddin su kayi nasara a kotu game da batun sunan jam'iyyar. A yayin da yake jawabi ga taron wasu mata a Abuja a ranar Juma'a, Galadima yace a yanzu APC ta tabarbare fiye ma da jam'iyyar PDP da ta hambarar daga mulki a shekarar 2015.
"Idan kotu tace mu ne shugabanin jam'iyya na gaskiya, zamu fitar da dan takarar shugabancin kasar mu," inji Galadima. "Abinda kawai muke bukata shine adalci da gaskiya da rashin bawa wasu fifiko, kuma a yanzu muna kalubalantar hanyoyin da aka bi wajen zaben 'yan kwamitin gudanarwa na jam'iyyar kuma da izinin Allah za muyi nasarar. "An zabe mu ne saboda munyi wa mutane alkawarin cewa zamu kyautata musu fiye da jam'iyyar data gabace mu amma a madadin hakan, mun fi su barna a yanzu. "Bamu amince duk wasu masu laifi su rika dawowa jam'iyyar mu ba har ta kai ga cewa APC ta zama jam'iyyar da wadanda ake tuhuma da laifukan rashawa ke shigowa don samun mafaka".



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments