PDP TA KAFA KWAMITIN CANJA SUNA DA INKIYA



- Rahotanni sun bayyana cewar jam'iyyar hamayya ta PDP ta fara yunkurin canja sunanta kafin zaben 2019
- Ta nada mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ya jagoranci kwamitin nemo sabon sunan da zata canja
- Jam'iyyar na son canja sunan ne domin kara samun damar lashe kujeru a zaben 2019




Wani sabon rahoto dake zuwa daga sansanin jam'iyyar adawa ta PDP na nuni da cewar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattijai Sanata Ike Ekweremadu domin nemo mata sabon suna.
Jaridar Thisday ta rawaito cewar, PDP na son canja sunanta ne biyo bayan asarar kujeru da take yi a zabukan da ake yi a fadin kasar nan. Rahoton ya kara bayyana cewar, PDP zata canja suna ne domin gujewa yawaitar alakanta sunanta da cin hanci da jam'iyyar APC mai mulki ke yi.
Canjin sunan na daga cikin dalilan da wasu 'yan APC, musamman tsagin R-APC, ke bukatar a yi kafin su shigo jam'iyyar ta PDP.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments