OBASANJO YA ZAMA MA’AIKACIN JAMI’AR DA AKE KARATU DAGA GIDA, NOUN
A ranar Talata ne tsohon shugaban
kasa Olusegun Obasanjo ya zama cikakken ma’aikacin jami’ar da ake karatu daga
gida wato wato National Open University of Nigeria, NOUN.
Obasanjo
ne dalibi na farko da jami’ar ta ba shaidar kammala karatun digirin-digirgir wato
Phd wanda bayan haka ta bashi aiki.
Obasanjo
zai yi aiki ne a ofishin makarantar dake jihar Ogun.
Mai
kula da aiyukan makarantar a jihar Ogun, Ibrahim Salawu, ya zazzagaya da
Obasanjo makarantar sannan ya nuna masa ofishin sa.
Obasanjo
ya jinjina wa jami’ar sannan kuma ya ce zai yi aiki tukuru domin ci gaban
jami’ar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku