MATSALAR TSARO: 'YAN SANDA SUNYI SA'AR KAMA MASU ADDABAR JAMA'A HAR 37 A SASSAN AREWACIN KASAR NAN


Hukumar Yan sandan Najeriya ta sanar da cewa jami'an tsa sunyi nasarar kama wasu gaggan 'yan fashi ga garkuwa da mutane guda 37 da suka addabi yankunan Arewacin Najeriya.









'Yan fashin wadanda suka kware wajen satar mutane da kuma satar motoci, sun dade suna addabar matafiya a yankunan jihohin Kaduna, Niger da Zamfara. Kakakin hukumar Yan sanda Jimoh Moshood ne ya gabatar dasu ga manema labarai a ofishin yan sanda da ke Suleja.
Moshood ya ce hukumar ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da sauke nauyinta na kare lafiya da dukiyoyin al'ummar Najeriya.




Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments