MARTANIN SHUGABA BUHARI KAN HUKUNCIN DA KOTU TA YANKE KAN BUKOLA SARAKI
A yau Asabar, shugaban Najeriya, Muhammadu
Buhari ya ce tabbas sashin shari'a na Najeriya yana aikinsa duk da cewa akwai
wasu kaluballe da yake fuskanta, ya kuma kara da cewa bai dace a bari wani
mahaluki ya kawo cikas ga sashin ba.
Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a yayin da yake
tsokaci kan hukuncin da kotun ta yanke na wanke shugaban majalisa Bukola Saraki
daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa a wata sanarwa da ta fito daga
mataimakinsa na musamman a fanin yadda labarai, Garba Shehu. A jiya Juma'a 6 ga
watan Yuli ne kotun koli da wanke Bukola Saraki daga tuhumarsa da kotun da'ar
ma'aikata tayi na yin karya wajen bayyana kadarorinsa.
Shugaba Buhari yace: "So da yawa naga
yadda wasu mutane ko kungiyoyi kanyi kokarin kawo cikas ga shari'a a tunanin
hakan ne zai tsiratar dasu a maimakon juriya da bin doka wajen jadada
gaskiyarsu. "Amma a shari'ar shugaban majalisa Bukola Saraki, na ga yadda
ya yi hakuri kuma ya jure dukkan wahalhalun da ke tattare da shari'a kuma daga
karshe kotu mafi daraja a kasa ta ce bashi da laifi. "Abinda nayi kenan
har sau uku a kotu a lokacin da aka zalunce ni kan sakamakon zabe har sai da
Allah ya bani nasara a karo na hudu. Yadda shugaban majalisar dattawar ya yi
hakuri da shari'ar tun daga kananan kotunaa har zuwa kotun koli babban darasi
ne ga yan Najeriya da ya kamata suyi koyi dashi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku