KOTU TA TSAYAR DA RANAR YANKEWA BAFARAWA HUKUNCI
A ranar Lahadi da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Sokoto,
Attahiru Bafarawa, ya kaddamar da takararsa ta tsayawa neman shugabancin kasa a
jam’iyyar PDP, har ya shaidawa manema labarai cewar Buhari dalibinsa ne a
siyasa.
Sai ga shi a yau laraba, Bafarawa, ya bayyana gaban babbar
kotun jihar Sokoto inda ake tuhumarsa da badakalar cin hanci ta kudi, biliyan
N15bn. Saidai rashin zuwan alkalin kotun, Bello Abbas, ya kawo tsaiko a zaman
kotun nay au. A ranar 8 ga watan Mayu ne mai shari’a Abbas ya tsayar da yau, 4
ga watan Yuli, a matsayin ranar da zai yanke hukunci a shari’ar da aka shafe
shekaru 9 ana fafatawa.
Saidai yayin zaman kotun na yau, lauyoyin wadanda ake tuhuma;
Bafarwa da Salihu Maibuhu – Gummi, ya shaida masu cewar alakalin ya yi bulaguro
domin gudanar da wani aiki, amma ya saka ranar 31 ga watan Yuli a matsayin
ranar da za a dawo domin sauraron hukuncin da kotun zata yanke.
Bafarawa na fuskantar tuhuma da 33 da suka jibanci cin hanci,
sayar da hannayen jarin gwamnati ba bisa ka’ida ba, almundahana, karbar kayan
sata, da kuma biyan kudi ba bisa ka’ida bag a wasu kamfanonin bogi yayin da
yake gwamna tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku