KOTU TA DAGE SAURARON KARAR JONAH JANG SAI BABA TA GANI
Kotu ta dage shari'ar
tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, wanda ake zargi da cinye Naira biliyan
6.3 zuwa 30 ga watan Oktoban wannan shekarar
Kotu ta dage shari'ar tsohon gwamnan jihar
Filato, Jonah Jang, wanda ake zargi da cinye Naira biliyan 6.3 zuwa 30 ga watan
Oktoban wannan shekarar. Jang, sanata ne mai ci a yanzu kuma yana gaban shari'a
ne karkashin mai shari'a Daniel Longji na babbar kotun jihar Filato a bisa
zargin shi da ake da laifuka 12 da suka hada da barnatar da dukiyar al'umma.
A tare da shi akwai daya daga cikin ma'aikatan
ofishin Sakataren Gwamnatin jihar, Yusuf Gyang Pam, wanda shima ake zargin shi
da amfani da kujerar shi gurin azurta kanshi da Naira miliyan 11.5. Jang dai ya
almubazzarantar da wasu kudade na musamman da babban bankin Najeriya ta tura
jihar shi don rabawa kanana da matsakaitan kasuwanci domin bunkasa su, ana
saura wata biyu ya sauka daga kujerar shi ta gwamnan jihar a shekarar 2015.
Shari'ar da aka yanke sauraron ta a yau 17 ga watan Yuli, an yanke hukuncin
dage ta ne saboda shaidun masu karar basu halarci kotun ba. Lauyan masu karar
ya roki mai shari'a da ya dage sauraron karar saboda rashin samun damar kawo
shaidar zuwa kotun sakamakon rashin tsaro a jihar. An dage shari'ar tare da
fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali zasu dawo jihar.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku