KOTU TA BADA BELIN SAMBO DASUKI


Kotun Koli ta Tarayya da ke zaune a Abuja ta ba da belin tsohon mai bada shawara kan tsaron kasa, Colonel Sambo Dasuki (Mai Ritaya ).

Wannan shi ne beli na shida da aka ba wa tsohon NSA. Duk da haka, ya kasance a tsare a gidan tsare masu laifi na (DSS).
Mai shari'a Ojukwu a ranar Litinin ta bayyana cewa, tsare Dasuki na tsawon shekaru biyu da rabi na iya kawo cikas ga dokar kasa da kuma lafiyar sa.
Saboda haka, ta bada belin Dasuki a kan Naira Miliyan Dari Biyu da Shaidu masu rattaba hannu domin belin sa guda biyu.
Masu belin sa dole ne su kasance Ma’aikatan gwamnati masu matsayi taku sha shida kuma wadanda suka mallaki Filaye ko gidaje a Asokoro, Maitama, Utako ko Garki a Abuja.
Har ila yau, ana sa ran kowane mai yin belin Dasuki, sai biya Miliyan dari wa kotu a matsayin kudin beli.
Saboda haka, ta umarci DSS cewa, idan hukumar na so ta yi hira da Dasuki a nan gaba, dole ne a yi ba tare da tsare shi ba, sa’an nan ya kasance ranar da ake  aiki.
A nasa bangare, tsohon Mai bada shawara ga Shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Dasuki ya roki kotu ta umarci DSS ta sake shi bayan shekaru biyu da rabi a tsare ba tare da fitina ba.
Ya kuma nemi kotun ta umarci DSS ta ba shi Naira biliyan biyar a matsayin babban hasara, da kuma Babban Mai Shari'a na Tarayya ya nemi gafara a wurinsa domin domin tsare shi da aka yi ba bias ka’ida ba.
Mai shari'ar ta ce, duk da cewa an bada belin Dasuki, Kotu baza ta iya bada daman bbiyan wani kudi ga dasuki a matsayin hasara ba.


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments