KO A GADON ASIBITI BUHARI YAKE ZAI CI SOKOTO, BAUCHI DA KANO -INJI AMAECHI



Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya yi kurin cewa Buhari zai lashe zabe a jihohin Kano, Bauchi da Sokoto ko da ko yana kan gadon asibiti ne.
Amaechi ya bayyana haka ne a hira da yayi da jaridar Punch.
Ya Kara da cewa tabbas gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwa da na Kwara, Abdulfatah Ahmed duk zasu koma PDP nan ba da dadewa ba.
“ Sokoto garin Buhari ce, bamu ko tantama akai. Buhari zai lashe Sokota tatas a 2019. Sannan kuma ko ‘yan majalisun da suka canza sheka duk sun fito ne daga wuraren da koda su ko basu Buhari zai ci zabe.
Amaechi ya ce idan dai mana ce ta 2019, Buhari ya ci ya gama.
Sai dai kuma a martini da tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya maida wa Amaechi yace wannan zancen gizo da koki ne.
Kwankwaso yace Buhari ba zai ci Kano ba a 2019, idan mafarki Amaechi yake yi toh ya farka.
Binta Sipikin da ta sakawa takardar maida martanin hannu tace ficewar Kwankwaso daga APC ba Kano ba kawai zata gurgunta, zai shafi jam’iyyar APC ce baki daya.
“ Idan ka zagaya kasar nan za ka ga cewa babu inda babu masoya Kwankwasiyya. Saboda haka abin bana wasa bane.
“ A haka ma kawai yana da miliyoyin magoya baya ballantana kuma sun hada karfi da tsohon gwamna Yanzu, Ibrahim Shekarau. Sannan ina so in tabbatar maka cewa ko menene gwamnati a Kano za tayi, na gaba yayi gaba, Buhari ba zai taba cin Kano ba.
Ko da yake a jiya Juma’a gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi kurin cewa Kano ta Buhari ce, babu wani da ya damu da ficewar Kwankwaso daga APC a Kano.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments