KEMI ADEOSUN: GWAMNATI TA MAYAR DA MARTANI KAN BATUN SATIFIKET NA KEMI ADEOSUN
- Kwana hudu da aka fara zargin bata yi bautaer
kasa ba
- Tayi kememe taki cewa komai
- Lai Mohammed yayi martani
Da 'yan jarida suka rutsa shi da tambayoyi kan
batun NYSC da aka bankado, da cewa wai bata yi bautar kasar ba, kuma ma
satifiket dinta na bogi ne, gwamnati ta mayar da martani kan batun, a zaman da
aka yi na dazu na majalisar kasa. A kokarin jin ta bakin sa, Lai Muhammed yace
bashi da ta cewa tunda gwamnati tayi bayani, kuma tace tana bincike.
Ya kara da cewa, hukumar NYSC, ita ma bangaren
gwamnati ce, kuma tace tana duba lamarin, don haka ba sai ya kara cewa komai
ba. In dai ta tabbata wannan batu haka yake, cewa qaga satifiket din tayi, dole
ne shugaba Buhari ya sauke ta, kuma tayi zaman gidan kurkuku.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku