KASAR CHINA ZATA YI WA NAJERIYA AGAJI DA RIGAKAFIN ZAZZABIN CIZON SAURO

- In dai maganin gargajiya ake magana, kasar Sin ta sanshi
- Magungunan zamani ma ba'a barta a baya ba
- Babu inda zazzabin sauro ke lahani a duniya irin Najeriya


Domin kawo karshen cutar nan mai hatsari ta zazzabin cizon sauro a Najeriya, masana a bangaren lafiya daga jami'ar Jiangxi ta magungunan gargajiya ta kasar China ta kawo sabon maganin cutar a Najeriya. A wani taro da akayi a Legas, wanda ya samu halartar shuwagabannin cibiyoyin gwamnati, masana daga China sunce sabon salon yaki da cutar ba wai da cutar zazzabin cizon sauro zai yi yaki ba, har da ma wasu cutukan da suka zamo barazana a Najeriya.
A lokacin da ake kwatanta maganin gargajiya na Chanis din a matsayin magani mafi inganci gurin yaki da kalubalen da ake fuskanta na lafiya, mataimakin shugaban masu duba marasa lafiya na China a Legas, Duan Zhongqi, yace zasu cigaba da hada kai da hukumomin Najeriya don cigaba da kawo ingantattun magunguna.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com


Comments