JAMI’AN ‘YAN SANDA SUN HANA SARAKI DA EKWEREMADU FITA DAGA GIDAJEN SU
‘Yan sanda tun da sanyin safiya
bayan Sallar asubahi suka hana Kakakin Majalisar Dattawa Bukola Saraki da
Mataimakin sa, ike Ekweremadu fita daga gidajen su.
Rahotannin da ke yawo tun jiya da
rana a Abuja sun tabbatar da cewa a yau ne ‘yan majalisar dattawa za su yi
fitar-farin-dango daga APC.
Hakan
kuwa na nufin kafin yammacin yau APC za ta koma jam’iyyar marasa rinjaye a
majalisa kenan.
Ana
ganin wannan ne dalilin hana shugabannin majalisar fita daga gida domin kada su
samu sukunin halartar zaman majalisar.
Kakakin
Saraki, Yusuf Olaniyonu ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Saraki ya sa an fita
da motoci waje domin ya halarci gayyatar da yan sanda suka yi masa a ofishin
SARS da ke Guzape, Abuja.
“Amma
‘yan sanda tuni sun gitta motocin su kuma sun jibge jami’ai kan titin kofar
gidan, sun hana kowa shiga ko fita.”
“Yanzu
haka da na ke maka magana ban iya fita waje, ina ciki.”
Shi
ma kakakin Ike Ekweremadu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda sun kewaye
gidan, sun hana shi fita.
“Ba
na jin zai iya fita a yau idan aka yi La’akari da yawan jami’an da aka jibge a
kofar gidan sai.”
Dama
dai jiya ne R-APC suka ce alkalami ya bushe, ba za su yarda a sasanta ba.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku