JERIN SUNAYEN ‘YAN MAJALISAR WAKILAI 37 DA SUKA FITA DAGA APC



Wani rahoto da muka samu da dumi dumi yanzun nan ya tabbatar da cewa akalla mambobin majalisar wakilan Najeriya 37 ne suka yi fatali da jam’iyyar APC mai mulki, suka kuma rungumi jam’iyyar PDP, ta adawa.
Daga cikin ‘yan majalisar 37 da suka fice, 33 ne suka koma PDP yayin da wasu 4 daga jihar Osun suka koma sabuwar jam’iyyar ADC ta Obasanjo. Ga jerin sunayen ‘yan majalisar da suka koma PDP din kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito;



Emmanuel Orker-Jev

Sani Rano

Barry Mpigi

Ali madaki

Dickson Tackighir

Hassan Saleh .

Danburam Nuhu

Mark Gbilah

Razak Atunwa

Ahmed Garba Bichi

Abdulsamad Dasuk

Zakari Mohammed


Canjin shekar ‘yan majalisar ta wakilai na zuwa ne bayan mambobi15 a majalisar dattijai sun canja sheka PDP din, duk a yau. Komawar ‘yan majalisar ya haifar da hargowa da hayaniya a zauren majalisar ta wakilai, dalilin day a saka ‘yan jam’iyyar APC ficewa daga zauren majalisar.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments