JAMI’AN TSARO SUN TARWATSA MAGOYA BAYAN PDP DAGA WAJEN GANGAMI




Jami’an tsaro sun tarwatsa magoya bayan jam’iyyar PDP daga filin gangamin da jam’iyyar zata yi gabannin zaben gwamna a jihar Ekiti.


Mambobin jam’iyyar sun taru a shahararren wajen shakatawar nan na Fayuyi dake Ado Ekiti, babban birnin jihar a ranar Laraba kafin a fara harbe-harben bindiga a sama.

Bayan nan, Gwamna Ayodele Fayose yayi yunkurin jagorantar magoya bayan zuwa filin taron sai dai hakan bai yiwu ba bayan jami’an tsaron sun sake harba bindiga a sama.


Hakan ya sa an juya akalar taron zuwa harabar gidan gwamnati inda aka sanya ran Gwamna Ayodele Fayose da sauran shugabannin PDP zasu yi jawabi ga mambobin jam’iyyar.



Comments