FOMWAN DA MEDA NA HORAS DA ‘YAN MATA MASU TALLA 50 SANA’O’I

Kungiyar FOMWAN ta mata musulmi a Nigeria tare da hadin guiwar kungiyar MEDA ta kasar Canada sun fara aikin horas da yara ‘yan mata masu talla guda 50 a garin Soro da ke karamar hukumar ganjuwa, Sanin yadda za su rika aiwatar da harkokin kasuwanci a waje guda ba tare da yawon tallace tallace ba. Shirin Wanda za a gudanar da shi na tsawon watanni biyar, zai ci gaba da horas da yara Yan mata yadda za su rika sarrafa waken soya da gyada da shinkafa ta hanyar gudanar da kasuwanci a waje guda ba tare da yawon talla ba. Hajiya Fatsuma Mohammed shugabar shirin ilmantar da matan ta gudanar da lacca ga ‘Yan matan a karon farko kan su himmatu wajen neman ilmin addini da na zamani ingatacce. Bayan haka ta hori matan su kasance masu lura da lafiyar su don samun ingancin rayuwa.

 Don haka ta bukace su da su kasance masu lura da kansu ta hanyar jinkinta lokacin yin aure har sai sun girma sun kai shekaru 18 don su kosa ta yadda za su samu sauki a lokacin da suka fara aihuwa. Hajiya Fatsuma Mohammed tashawarci matan kan su san hanyoyin da za su rika kare rayuwarsu daga barazanar shiga mummunan yanayi da ke gurbata rayuwa. Musamman a wannan lokaci da ake samun yawaitar fade a lokacin da aka fita neman abin rufin asiri. 

Don haka ta bukaci yan matan su lura da tsabtar jikin su da ta muhalli da kuma yadda suke gudanar da rayuwa cikin taka tsan tsan. Don haka ta bukaci yaran su lura da rayuwa wajen yin karatu na zamani da na addini cikin kiyaye hakkokin su da rayuwar su ta hanyar kula da tarbiyyar kan su da kuma yin taka tsan tsan wajen neman abin Kansu ta hanyar tsugunawa a waje guda don inganta neman abin kan su ba tare yawan tafiya ywon talle ba saboda a wasu lokuta ana gamuwa da hatsari. Taron ya mayar da hankali wajen koyawa Yan matan yadda za su lura da Kansu da kuma yadda za su nemi ilmin zamani don amfanin kansu da na zuriyarsu. Fadar Sarkin Soro ne ta taimaka wajen halara Yan matan a makarantar firamare ta Soro north don gudanar dantaron bitar wanda Yan matan suka bayyana gamsuwa da abin da suka koya kamar yadda shamsiyya Musa ta bayyana a lokacin da suka yi aikin hadaka an wajen taron.





DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments