FAYOSE YA FASHE DA KUKA YA CE JAMI’AN YAN SANDA SUN MARE SHI SANNAN SUKA HARBE SHI
Gwamnan jiar Ekiti,Mista Ayodele Fayose, ya ce
jami’an yan sanda da aka turo jiharsa don zaben gwamna da za’a yi a rana Asabar
sun kai farmaki inda jam’iyyar PD ke gudanar da ganganminta sanna suka ci
zarafinsa.
Gwamnan wadda aka gani sanye da wani abun tare
wuya ya koro bayanin halin day a shiga sannan ya bukaci magoya bayan jam’iyyar
da su jajirce sannan su zabi mataimakinsa wadda shima dan taarar gwamna ne a
lemar PDP, Farfesa Olusola Kolapo.
Fayose wadda ya fashe da kuka yayinda yake
zantawa da manema laarai ya ce jami’an yan sanda su mare shi sannan suka
zungure shi tare da harbin sa.
Fayose ya kuma bayyana cewa duk abun day a same
shi toh babu wanda za’a kama sai sufeto janar na yan sanda.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku