DINO MELAYE YA BAYYANA YADDA YA TSERE A HANNUN WADANDA SUKA SACE SHI



A jiya Alhamis ne rahotanni ta kafun yada labarai suka nuna cewa wadansu ‘yan  bindiga sun yi nasarar sace Sanata Dino Melaye. Rahotanni a jiyan sun nuna cewa an sami bayanin faruwar lamarin ne ta shafin tiwita inda Sanata Ben Murray Bruce ya sanar cewa dan uwan Sanata Dino ne ya sanar da shi cewa an sace shi a hanyarsu ta zuwa kogi domin amsa sammacin da kotu tayi masa.
Abin da ban mamaki kuma da alaman tambaya.
Domin a yau Juma’a ne shi Sanata Dino Melaye yayi ruwaito a shafinsa na Tiwita cewa ya gode wa Allah domin yayi nasarar tserewa daga hannun wadanda suka sace shi a jiya. Sai dai babu cikakken bayani game da yadda ya tsere daga hannun tasu.

Yaya jama’a zasu bayyana wannan lamarin?
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments