BUHARI YA TAUSAYAWA WADANDA TASHIN GAS YA CIKA DA SU A KADUNA


Sakon shugaban kasar na kunshe ne a wata sanarwa daga babban hadiminsa, Mallam Garba Shehu, a Abuja a ranar Lahadi.



Shugaban kasar yace yana jin radadinsu a wannan mawuyacin lokaci, da kuma lura da asarar tattalin arziki wanda yan Najeriya masu kwazo suka gina don ganin sun rayu cikin kwadago na gaskiya. Ya kara da cewa: “A matsayina na mutum, ina sane da asarar da wannan hatsari ya janyo a rayuwar wadannan yan Najeriya masu kwazo.”


Shugaban kasar ya shawarci yan Najeriya da su mayar da hankali sosai wajen kula da bin matakan da suka dace a haraban kasuwancinsu. A cewarsa, mayar da hankali wajen kula da matakan zai taimaka matuka wajen kore duk wata annoba da zata taso.

A baya mun ji cewa a yammacin ranar Asabar gas ya tashi inda ya kona shaguna 14 da wani dakin hada magunguna inda wani mutum daya ya ji rauni a hanyar Ibrahim Taiwo Road dake unguwar Abeokuta a Kaduna. 




Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments