BUHARI YA JAJANTA WA ‘YAN KASUWAR TERMINUS A JOS, JIHAR FILATO
Shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari ya jajanta wa al’ummar jihar Filato kan mummunar gobarar da ta lakume
shaguna sama da 200 a kasuwar Terminus da ke birnin Jos, in da ya ce, ya kadu
da wannan ibtila'in.
Wata sanarwa da mai
taimaka wa Buhari kan harkokin watsa labarai, Garba Shehu ya fitar ta ce,
shugaba Buhari ya ce, ya kadu matuka da wannan ibtila’in da ya haddasa asarar
dukiya mai tarin yawa.
Buhari ya kuma nuna
damuwa kan cewa, a karo na uku kenan cikin shekaru 10 da irin wannan gobara ke
barna a wannan kasuwa.
Shugaban ya kuma bukaci
hukumomin da ke da ruwa da tsaki da su dauki matakan da suka dace wajen hana
yawaitar aukuwar gobarar.
A yayin zantawa da
sashen hausa na RFI, shugaban 'yan kasuwar Alh. Mustapha Ibrahim Bako ya ce,
yanzu haka suna kan gudanar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar wadda
ta fara tun da misalin karfe 1 na dare a ranar Jumma’a.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku