BUHARI YA AIKA DA DAKARUN NAJERIYA 1000 DA JIRAGEN YAKI JIHAR ZAMFARA
Shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya bada umarnin a aika zaratan dakarun Najeriya 1000 da
jiragen sama na yaki jihar Zamfara domin gamawa da tsagerun ‘yan ta’adda da
suka addabi mutanen jihar.
Wadannan dakaru sun
hada da jami’an ‘yan sanda, Sojoji, Sibil difens, da sojojin sama.
A takarda da kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya
saka wa hannu ya ce tuni har babban hafsan sojojin saman Najeriya Abubakar
Saddique ya isa garin Gusau inda ya tattauna da mataimakin gwamnan jihar ranar
Lahadi.
” Gwamnati ta dauki
dan tsawon lokaci ne don a samu na’urar gano inda wadannan ‘yan ta’adda ke boya
da kuma samar da manyan makamai domin tunkarar su.
Jihar Zamfara ta yi
kaurin suna kan ayyukan ta’addanci, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da
sauran su.
An sace dubban shanu, an kashe mutane masu dinbin
yawa sannan an kona kauyuka da dama a sanadiyyar ayyukan wadannan ‘yan ta’adda.Jiragen saman yaki da zasu yi aiki a wannan yankuna zasu na tashi ne daga filin jirgin sama dake Katsina.
Buhari ya kuma yi kira da a daina maida harkokin
tsaron kasa siyasa.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku