BUHARI DA SHUGABAN KASAR AFRIKA TA KUDU SUN SAKA LABULE A FADAR GWAMNATIN NAJERIYA


A jiya, Laraba, ne shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, da takwaransa na kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, suka yi wata ganawar sirri a fadar gwamnatin Najeriya dake Abuja.

Shugaba Buhari ya tarbi Ramaphosa bayan isowarsa fadar gwamnatin Najeriya, Villa, da misalign karfe 3:00 na rana. Shugabannin biyu sun tattauna batutuwan game da suka kasashen da suke shugabanta, musamman batun tattalin arziki da tsaro. A ranar 8 ga watan Yuli ne fadar shugaban kasa ta koka a kan yawaitar hare-hare da ake kaiwa ‘yan Najeriya dake zaune a kasar Afrika ta Kudu bisa wasu dalilai marasa ma’ana.


Mai taimkawa shugaba Buhari a bangaren harkokin kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana rashin jin dadinta bisa salwantar rayukan ‘yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu.




Kamfanin sadarwa na MTN, mallakar kasar Afrika ta Kudu, na fuskantar tirjiya da zanga-zanga daga ma’aikatansu da kungiyar kwadago ta Najeriya a kan rashin mutunta ma’aikata da kulawa da hakkokinsu. Shugaba Ramaphosa dake ziyarar aiki a Najeriya, zai kasance bako na musamman a taron habaka cinikayya tsakanin kasashen Afrika karo na 25 dake gudana a Abuja.




Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com 

Comments