AN SACE WANI LIMAMIN COCI A JIHAR KOGI



Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a tabbatar da su waye ba sun sace babban limamin cocin Catholica na St. Michael, a Obajana dake jihar Kogi, mai suna Rev. Fr. Leo Michael



Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a tabbatar da su waye ba sun sace babban limamin cocin Catholica na St. Michael, a Obajana dake jihar Kogi, mai suna Rev. Fr. Leo Michael. Wani babban Fasto na cocin Catholic Diocese, Rev. Fr. Peter Adinoyi, shine ya bayyanawa manema labarai afkuwar lamarin a garin Lokoja yau dinnan.

Ya ce Faston yana dawowa daga Okene zuwa Obajana a lokacin da aka sace shi din, a dai dai Kauyen Irepeni dake kan hanyar Okene zuwa Lokoja. A cewar shi an gabatar da rahoton sace limamin ga ofishin 'yan sanda na kauyen Irepeni. Bayan haka, Adinoyi ya ce a ranar 25 ga watan nan 'yan bindigar sun kira mambobin cocin limamin, inda suka bukaci a basu naira miliyan 50, kafin su saki Faston. 

Ya ce daga baya sun rage kudin zuwa miliyan 20, har ya dawo miliyan 8. Adinoyi ya ce 'yan bindigar sun bawa mambobin cocin zuwa karfe daya na ranar yau akan su gabatar da kudin ko kuma suki sakin Faston. Ya ce mutanen cocin sun kasa hada kudin, inda suka kira hukumar tsaro akan su taimaka wurin ceto rayuwar limamin.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments