BINCIKE YA NUNA CEWA NAJERIYA NA BUKATAR MA’AIKATAN KIWON LAFIYA 450,000 DUK SHEKARA
Najeriya na bukatar ma’aikatan kiwon lafiya 450,000 duk shekara
kafin ta iya samar da ingantaciyyar kiwon lafiya ga mutanen kasar nan.
Jami’in kungiyar ‘Development Research and Project Center
(dRPC)-PAS’ Emmanuel Abanida ya bayyana haka in da ya kara da cewa sai an dauki
ma’aikata 450,000 duk shekara aiki a fannin kiwon lafiya kuma na tsawon shekara
10 cur kafin a sami natsuwa a harkar kiwon lafiyar kasar nan.
Abanida ya fadi haka ne a taron da kungiyoyin ‘development
Research & Project Center (dRPC)’ da ‘Partnership for Advocacy in Child and
Family Health (PAS) project’ ta shirya domin tattauna rawar da kungiyoyi masu
zaman kan su za su iya takawa wajen samun nasarar shirin Muradin karni (MDGS) a
kasar nan wanda aka yi a Abuja a makon da ya gabata.
Shirin Muradin karni da suka shafi kiwon lafiya da wadannan
kungiyoyi ke aiki a kai sun hada da inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana,
kawar da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro,tarin fuka da sauran cututtuka da
ake fama da su a kasar nan.
Abanida ya kara da cewa rashin ma’aikata a fannin kiwon lafiyar
Najeriya ya zama tsohon labari domin kuwa a yanzu haka adadin yawan ma’aikatan
dake aiki a fannin ba su wuce 45,000 ne kawai.
” Bincike ya nuna cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen
yankin Afrika dake fama da karancin ma’aikatan jinya da ungozoma daga nan sai
kasar Ethiopia ke biye da ita.
” Bincike ya kara muna cewa kashi 65 bisa 100 na mutanen kasar
nan ne ke samun kula na kiwon lafiya luma kashi 70 na mazaunan karkara na ba su
samun kula kamar yadda ya kamata na lafiyar su.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku