APC - GWAMNONI DA MINISTOCI ZASU BAWA BUHARI MAMAKI - GALADIMA
Kwanaki biyu bayan wasu daga cikin 'ya'yan
jam'iyyar APC sun ware kansu daga uwar jam'iyyar saboda rashin gamsuwa da yadda
ake tafiyar da harkokin jam'iyyar, shugaban sabuwar APC din, Buba Galadima ya
furta cewa wani abinda zai razaka jam'iyyar APC na nan tafe. Galadima ya yi
zargin cewa mutane da yawa da ke kusa da shugaba Muhammadu Buhari suna da hannu
dumu-dumu cikin rashawa. A hirar da ya yi da Saturday Sun, Buba wanda dan aslin
jihar Yobe ne kuma tsohon aminin shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai wasu Gwamnoni
da Ministoci masu ci yanzu da zasu shigo sabuwar jam'iyyar ta APC.
Ya bayar da misali da yadda wasu kusoshin
jam'iyyar ta APC a jihar Kwara suka fice daga jam'iyyar inda ya kara da cewa
za'a samu karin masu ficewa daga wasu jihohin. Sai dai bai fadi rannan da
wannan abin mamamkin zai faru ba. A wata rahoton, NAIJ.com ta kawo muku cewa
shugaban na sabuwar APC wanda suka hada kai da 'yan bangaren sabuwar PDP yace
suna da karfin da yawa a majalisar tarayya da za su iya tsige shugaba Muhammadu
Buhari idan hakan ta kama. Galadima ya mayar da martani kan kalaman shugaban
APC na kasa, Adams Oshiomole inda ya yi ikirarin cewa mutanen dake da rAPC basu
da wani muhimmanci, yace wanda ke adawa dasu ne basu da nagarta. Injiniya
Galadima wanda yana cikin amintattun jam'iyyar APC kuma tsohon jigo a jam'iyyar
CPC, ya yi kira ga 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata su goyi bayan
sabuwar jam'iyyar nasu. Jam'iyyar ta rAPC da aka kafa kwananan ne dan nufin
ceto 'yan Najeriya daga kangin da suke shiga.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku