ZAZZABIN LASSA: WANI LIKITA YA RASU



Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta ruwaito cewa cutar zazzabin Lassa ta bullo a jihar Edo inda cutar ta yi ajalin wani Likita wanda ma’aikacin jinya ne a asibitin kamfanin yin manja ‘OkomuOilPalm Company’.
” Majiyar mu ta fada mana cewa tun a makon da ya gabata ne shi wanda ya rasu din mai suna Henry ke kwance a wannan asibiti sannan gwajin da likitoci suka yi a kan sa ya nuna cewa zazzabin cizon sauro ne ya kamu da.
” Da zazzabin ya ki ci yaki cinyewa sai asibitin ta gwada jinin Henry a wani asibiti mai zaman kan sa, a nan ne suka gano zazzabin Lassa ne ya kama shi. Sai dai kafin a dauke shi a tafi dashi asibiti da ake kula da masu wannan cuta ya ce ga garinku nan.



Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments