ZANGA-ZANGA NA IYA KAWO TSAIKO GA AYYUKA A MAJALISAR DOKOKI
Domin nuna adawa ga sharuda 12 da majalisar
dokoki ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika, wata kungiyar al’umma
na yunkurin gudanar da zanga-zanga a harabar majalisa a Abuja, wanda ka iya
durkusar da ayyukan yan majalisa a ranar Talata
A makon da ya gabata ne majalisar dokokin
kasar, ta gindayawa shugaban kasa Buhari wasu sharuda 12 da take son yayi aiki
a akai, bayan wata ganawa tsakanin majalisar dattawa da na wakilai inda yan
majalisan suka yi barazanar tsig shugaban kasar idan yake aiki akan sharudan.
Majiyoyi daga majalisar dokokin a jiya sun ce suna sane da shirin zanga-zanga
da wata kungiya jama’a ke yi a ranar Talata, sannan kuma sun yi gargadin cewa
idan aka bari hakan ta kasance babu abun da zai haifar sai ma gurguntar da
ayyukan majalisar.
Anyi zargin cewa an dauki nauyin kungiyoyin ne
domin su yi zanga-zanga akan majalisar dokoki tare da shugaban majalisar
dattawa Bukola Saraki a matsayin mutun na farko da za’a kaiwa hamayya
Kungiyar Dynamic Patriotic Citizens Group, ta
hannun babban sakatarenta na kasa, Shehu Mohammed tayi zargin cewa an tanadarwa
kungiyoyin dake shirin yin zanga-zangar tsaro damusamman daga sama. A halin da
ake ciki, Sabuwar PDP kungiyar adawar APC ta bayyana cewa tana jiran jam’iyya
mai mulki da shugaban kasa Muhammadu Buhari suyi kira gare su, sannan kuma ta
tunasar da jam’iyyar cewa lokaci na shirin kure masu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada
zumunta
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku