ZAN IYA FATATTAKAR BUHARI DAGA ASO ROCK – KWANKWASO
Tsohon gwamnan jihar Kano sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana
cewa babu abin da zai hana jam’iyyar PDP fatattakar Buhari daga Aso rock a
2019.
Kwankwaso ya fadi haka ne a hira
da yayi da Dele Momodu, sannan ya kara da cewa tabbas idan shi da jam’iyyar PDP
suka hade zasu kada Buhari cikin ruwan sanyi ma.
” Ni yanzu ina nan ga mai rabo
ne, Jam’iyyar PDP ce kawai zata iya kada APC saboda tana da girma da mabiya.
Abi daya da zai iya kawo musu baraka shine idan suka yi karfa-karfa wajen fidda
dan takaran shugaban kasa.
” Dole a zabi dan takara daga
jihohin nan uku da ake kira 3K wato Kaduna, Kano da Katsina, domin nan ne
kuri’u suke. Zai yi wuya wani ya yi nasara ko tasiri a zabe idan ba daga wannan
yanki yake ba.
Shi dai sanata Kwankwaso ya na
zaman doya da manja ne da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje sannan tuni ya
nuna baya muradin jam’iyyar APC kuma kwata-kwata.
“Zan iya komawa PDP, sai dai fa idan
ba su gyara gidan su ba musamman wajen zaben dan takara, za a koma gidan jiya
ne kawai.
” Zan iya tabbatar musu cewa zan
kada Buhari idan aka zabe ni dan takara a PDP.”
Sai dai kuma wani jigo a
Jam’iyyar APC Ayo Akanji ya yi watsi da barazanar da Kwankwaso yayi cewa zai fi
Buhari tasiri a 2019.
” Dama can mun sani cewa zai fice
daga APC, idan ya gama yin shawara, ” umma ta gai da Indo.”
” Farin Jinin Buhari a Kano ba
shi da na biyu. Idan Lokaci yayi zai fito da nasa dabarun da jama’ar sa muma
namu za mu fito a goge raini. Ga fili ga doki, a nan ne ‘yar fara zata nuna, ay
Kwankwaso bai ishemu kallo ba ma. A zuba a gani” Inji Akanji.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku