‘YAR MARIGAYI MKO ABIOLA TA BAYYANA CEWAR TSOHON SHUGABAN KASAR NAJERIYA OBASANJO BAI CI ZABEN SHEKARAR 1999 BA A NAJERIYA



Tudun Abiola, diyar marigayi MKO Abiola ta bayyana cewar tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo bai ci zaben shekarar 1999 ba a Najeriya tare da bayyana cewar an dora shi ne a kan mulki kawai domin a kwantar da hankalin Yarabawa a kan abinda aka yiwa mahaifin ta.
Tudun ta kara da cewar, sojoji ne suka dasa Obasanjo a kan mulki domin ragewa ‘yan kabilar Yoruba radadin soke zaben Abiola na shekarar 1993. “An dora Obasanjo ne kawai a kan mulki, ba zaben sa aka yi ba. Ba a yi zabe a shekarar 1999 ba, kawai an yi rantsuwa ne,” Tudun ta shaidawa gidan Talabijin na Channels.


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments