WATA KARUWA TA YAYYAGA WA WANI ‘DAN SANDA KAYA SANNAN TA GALLA MASA CIZO



Wadda ake tuhumar, wadda jami'an yan sandan suka bayyana a matsayin karuwa sun ce ta takale su da fada ne saboda sun yi kokarin kama ta. ‘Yan sandan sun bayyanawa kotun cewa, yarinyar ta yaga kakin guda daga cikinsu inda kuma ta ciji dayan a lebbansa a lokacin da yayi yunkurin sanya ta a cikin motarsu ta farautar masu laifi. Sun ce sai da suka hadu har su uku a sannan ne suka samu damar kama ta har suka kaita ofishinsu, wanda daga nan ne aka gurfanar da ita a kotun majistiri ta Isolo wanda kotun kuma ta bada umarnin a tsare ta a gidan kaso.
Wannan al'amari ya faru ne a Otel din Okota dake jihar Legas, wanda a nan ne wannan matashiya ke yin sana'arta ta karuwanci. ‘Dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana Kotun cewa, matashiyar ta samu saɓani ne da wata abokiyar sana'arta wanda har ta kai ga ta dauko reza tana mata barazana da ita. An yi kokarin ganin an kawo karshen rikicin amma abin ya ci tura wanda daga nan ne aka bugawa jami'an yan sanda waya, suka zo suka kama ta.

Alkalin kotun ta bada belin ta akan kudi Naira dubu 100,000 bisa sharadin kawo wanda zai tsaya mata, amma kafin lokacin, alkalin ta tisa keyarta zuwa gidan kaso har sai ta cika wadannan sharuda sannan za a sake ta. Kana daga bisani ta ɗage karar zuwa 26 ga watan Yuli na shekara ta 2018



Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments