WATA BABBAR MOTAR TANKA TA KAMA DA WUTA A GADAR OTEDOLA DAKE WAJEN LAGAS.
Wata babbar motar tanka ta kama da wuta a gadar Otedola dake
wajen Lagas. An tattaro cewa hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Lagas
(LASEMA) da hukumar kashe gobara na jihar Lagas na wajen da abun ke afkuwa.
Rundunar yan sandan mai yaki da yan fashi wato SARS ce ta bayyana hakan ta
shafinta na Twitter @rrslagos767.
Hukumar RRS tace jami’anta na kasa domin magance lamarin.
A cewar shaidu da abun ya afku a idanunsu, sunce wutan ya
lashe sama da motoci 20 da kuma wasu mutane da ba’a san adadinsu ba akan gadar
ta Otedola, babban titin Lagas zuwa Ibadan.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku