WASAN NAJERIYA DA ARGENTINA: WASA MAI TSANANI


'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya sun shawarci Super Eagles da su buga wasan da ta dace da Argentina a yau Talata.
Peter Bewarang, Mai kula da masana’anta na Hukumar kwallon kafa ta kasa ta NFF, Taiwo Ogunjobi, tsohon sakatare janar na NFF, yace Super Eagles bata da wata hujja ko dalili da zai hana ta cin Argentina.
A cikin ganawar da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin a St. Petersburg a Rasha, Bewarang ya amince da cewa Eagles na iya cin Argentina kai tsaye ba tare da shakku ba, domin irin nasarar da suka samu na cin Iceland, ci biyu masu ban haushi.
Najeriya zata kara ne da Argentina a yau Talata a St. Petersburg a wasan karshe na rukuni na D a gasar cin kofin duniya ta FIFA a 2018 a Rasha.
"Ya kamata su sani cewa idan har suka kasa cin Argentina a wannan wasan, To, nan take zasu koma gida, don haka su yi kokarin kada Argentina domin samun zarafin buga wasan rukuni nag aba "in ji shi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Nijeriya na da maki uku, idan suka fitar da Argentina ko suka yi kunnen doki a gasar, zai basu damar shiga zagaye na biyu na wasan cin kofin duniya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments