WANI UBA YA YI WA DIYARSA MAI SHEKARA DAYA (1) FYADE
Wata kotun majistare dake zaman ta a Ikeja ta jihar Legas tayi umarnin a tsare wani magidanci mai shekaru 36 a gidan yari na Kirikir bisa zargin sad a aikata laifin fyade ga diyar cikin sa mai shekara daya kacal a duniya.
Lalataccen mahaifin, Olaitan Adewoye, zai kasance a gidan yari na Kirikiri na tsawon kwanaki 21 kafin darektan sashen kula da kararraki na jihar Legas ya bayar da shawarar matakin day a kamata a dauka a kan mutumin bayan y agama nazarin takardun tuhumar da ake yi masa. Dan sanda mai gabatar da kara, Christopher John, ya shaidawa kotun cewar, Adewoye, mazaunin gida mai lamba 10 dake kan titin Arogundade dake rukunin gidajen Harmony a unguwar Ajah a garin Legas, ya aikata laifin ne ranar 17 ga watan Mayu.
Dan sanda John ya sanar da kotun cewar, Adewoye ya yiwa diyar ta sa fyade ne bayan mahaifiyar shi da yarinyar a gida tare da shaidawa kotun cewar mahifiyar yarinyar ta gano hakan ta faru ne bayan ta kai yarinyar asibiti domin a duba abinda ke damun ta saboda yawan kuka da take yi da an motsa ta.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku