WANI SOJA YA HARBE KANSA HAR LAHIRA




Wani kaftin din sojan Nijeriya a karkashin rundunar yaki da Boko Haram ta ‘Lafiya Dole’, ya dana wa cikin kunamar bindigar da yake aiki da ita, inda nan take ya bude wa kan sa wuta; daraam! Wannan al’amari ya afku ne a ranar 18 ga wannan wata na Yuni, a cibiyar kula da majinyata ta 7 Dibision Medical Centre, da ke Maidugurin jihar Borno. A yayin da aka kai sojan domin duba lafiyar sa a wajen. A cikin wasu bayanai da wata jarida mai yada labarai a shafin sada zumunta ta bayyana, ta ce an sakaya sunan sojan bisa zargin ko har yanzu mahukunta a gidan barikin basu shaida wa iyalan sa ba. Sajan wanda aka turo shi daga Barikin soja ta 22 Armoured Brigade, da ke Ilorin zuwa yankin arewa maso-gabas, yaki da Boko Haram. Kafin wannan sojan ya hallaka kan sa, wasu bayanai sun nuna cewa, da farko ya yi barazanar dirka wa mai kula da shagon da ake ajiye magunguna a barikin, ta hanyar tsallake rijiya da baya. Wanda a daga bisani, Kaftin sojan ya bindige kan sa, inda kan ka ce kwabo rai ya yi halin sa. Bugu da kari, jami’in sojan wanda yake aiki da rundunar dake karamar hukumar Mafa, a jihar, Borno, babbar cibiyar Boko Haram. Duk da har lokacin kammala wannan rahoton, jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaro a barikin 7 Dibision, bai ce uffan dangane da lamarin ba- a sakon kar ta kwana da daren ranar Laraba, har zuwa wayewar garin ranar Alhamis. Ko a kwanan baya, wani sojan Nijeriya ya takarkare tare da dirka wa abokin aikin sa yayan dalma, a garin Cibok da ke jihar Borno, duk da alwashin da rundunar tsaron ta dauka na gudanar da bincike.



Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments