TSUNTSAYE SUNA ZUWA KALLON WASAN CIN KOFIN DUNIYA
Bisa al’ada, magoya baya ne kan yi dandazo domin mara wa ‘yan wasansu baya a duk lokacin da suke buga wasan kwallon kafa to amma a wasu lokutan a kan samu wasu halittu da kan kai ziyarar ba-zata a lokacin da wasa ke gudana. Irin haka ne ya faru a wasan da aka buga tsakanin kasar Spaniya da Iran, a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ke gudana a Rasha. A wannan lokaci an tsinkayi wani karamin tsuntsu a cikin fili ‘yan wasan Spaniya biyu ne suka raka tsutsun zuwa gefen fili bayan da suka tsaya a filin suka ki fita kuma ana dab da fara buga wasan. Shahararrun yan wasa, Gerrard Pikue da Isco ne suka dauki tsutsun a hankali suka fitar da shi daga cikin filin wasan. Gerrard Pikue, wanda wannan ne karo na 100 da ya buga wa kasarsa Spaniya wasa, ya duka ya dauki tsuntsun da niyyar fitar da shi, amma sai tsuntsun ya tashi daga hannunsa, ya sake dawo wa cikin fili. Daga nan ne shahararren dan wasan Real Madrid, Isco, ya sake daukar tsuntsun a hankali zuwa wajen fili.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku