TIRELA YA YI KARO DA TANKAR MAI A HANYAR SULEJA-MINNA





Wani hatsarin wuta ya afku a ranar Juma’a, 29 ga watan Yuni a Malankaro, hanyar Minna zuwa Suleja bayan wata mokar tanka da tirela sun kara. Kakakin hukumar kare hatsarurruka a hanya, FRSC, Mista Bisi Kazeem ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne da safe. Ya kara da cewa jami’an hukumar kashe gobara dad a na FRSC sun kasance a wajen domin kashe wutan yayinda motocin ke konewa.
Idan ba zaku manta ba a daren ranar Alhamis, 28 ga watan Yuni ne wuta ya tashi a babban titin Lagas zuwa Ibadan inda motoci 54 suka gone, yayinda mutane tara suka mutu, hudu suka ji rauni.

 


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments