RIKICIN JIHAR PLATEAU: AN SANYA DOKAR TA BACI A JIHAR PLATEAU
-
Jihar Plateau na fuskantar barazanar barkewar rikici
-
Rikicin ya fara ne da karamar hukuma daya amma yanzu sun zama Uku
-
Dokar hana zirga-zirgar zata ke aiki ne daga 6pm na yamma zuwa 6am na safe
Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dukar hana zirga-zirga daga
magariba zuwa asuba a kananan hukumomi uku na jihar biyo bayan yaduwar rikici
daga karamar hukumar Barikin Ladi zuwa Jos ta kudu da yammacin yau Lahadi.
Daga baya rikicin ya yadu zuwa yankin Daffo da Kuba dake
karamar hukumar Bokkos. Rikicin ya samo asali ne tun a ranar Asabar tun bayan
da wadansu da ake kyautata zaton makiyaye suka kai wasu kauyuka inda suka kashe
mutane 11.
Hakan ta sanya wadansu suka fara zanga-zangar kin amincewa
daga bisani suka dauki doka a hannunsu inda suka tare babbar hanyar Jos suna
dukan motoci wanda hakan yayi sandiyyar haddasa haddura ga matafiya hanyar.
Dokar dai za tayi aiki daga yau da misalin 6pm na yammaci
inda kowa zai shiga gidansa ba tare da ya leko ba har zuwa 6am na safe, sai dai
kawai wadanda suke aiki na musamman mai muhimmanci. Mai magana da yawun
rundunar ‘yan sanda na jihar Terna Tyopev ya tabbatar da faruwar gudanar da
zanga-zagar a wani sakon karta kwana, amma ya bayyana cewa an aike da jami ‘an
‘yan san don shawo kan matsalar. Gwamnan jihar Simon Lalong da yake wurin taron
zaben shugaban jam’iyyar APC na kasa yayin al’amarin ya afku, yayi saurin katse
halartar taron domin dawowa gida don fara lissafin yadda za’a shawo kan
matsalar. Kamar yadda wani jawabin da ya fito daga kwamishinan yada labaran
jihar Yakubu Dati. Gwamna Lalong ya bukaci jami’an tsaro a jihar da su ribanya
kokarinsu don ganin an magance yawaitar kai hare-hare da ake yi kauyuka a
jihar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku