NIJERIYA TA BAMU WAHALA –MESSI
Kasar Argentina ta yi nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar neman kofin
duniya da ke gudana a Rasha, bayan doke Nijeriya ci 2-1 a karawar da sukayi a
birnin Saint Petersburg a yammacin ranar talata.
Dan wasan Argentina Lionel Messi ne ya zura kwallon farko a ragar
Nijeriya a daidai mintuna na 14 da fara wasan, kafin daga bisani dan wasan
Super Eagles Bictor Moses ya rama wannan ci ta hanyar bugun penareti a minti na
51, wannan dai na nufin cewa an fitar da Nijeriya daga gasar ta bana
Keftin na kungiyar kwallon kafar Nijeriya Mikel Obi, wanda ke zantawa da
manema labarai jim kadan bayan kammala wasan, ya ce ya yi matukar mamaki a game
da yadda alkalin wasan ya ki hura fenariti duk da cewa dan wasan Argentina
Marcos Rojo ya taba kwallon da hannunsa a mintuna na 76 da fara wasa kuma a
daidai farfajiyar kusa da mai tsaron raga.
Lionel Messi, ya ce tabbas Argentina ta yi nasara, amma ba ya tsammanin
cewa ya taba buga wa kasar shi wasan da ya ba shi wahala kamar wanda suka buga
da Najeirya a ranar ta talata ba.
Ya ce da farko sun kasance a cikin fargaba biyo bayan rashin samun
kyakkyawan sakamako a wasanni biyu da suka buga a baya, na biyu kuwa shi ne
yadda wasansu da Nijeriya ya kasance mai zafi fiye da yadda ake zato.
Mai horas da ‘yan wasan Nijeriya Gernot Rohr, ya ce tabbas ya yi nadama
a game da rashin samun nasarar Super Eagles, to sai dai ya ce ‘yan wasan sun
taka gagarumar rawa musamman bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, inda ya
ce matukar dai ‘yan wasan Super Eagles suka cigaba da kasancewa a hakan, to
lalle Nijeriya na da kyakkyawan fata a cikin shekaru 4 masu zuwa.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku