NAJERIYA DA ARGENTINA: OSINBAJO YA AMINCE DA NASARAR DAGA SUPER EAGLES
Mataimakin
Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Super Eagles za ta ci nasara da
takwaranta na Argentina don komawa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya ta
FIFA a Rasha.
Osinbajo ya bayyana
hakan yayin da yake magana da manema labaru a yau Talata a filin jirgin saman
Alakia a Ibadan.
"Ta wurin alherin Allah, nasara za ta zama namu. Ina fata ‘yan wasan mu za su ba kowa mamaki. Na tabbata kuma ina da tabbacin cewa sun shirya sosai don taka muhimmin rawa.
"Wannan wani muhimmin taro ne a gare mu, kuma ina bada gaskiya zai kasance babban nasara a gare mu", inji shi.
Hukumar Labarai ta Najeriya ta bayyana cewa Eagles za ta kara da Argentina a wasan rukunin D na rukuni na biyu a gasar cin kofin duniya kuma suna bukatar nasara a wannan wasa don cancantar zagaye na biyu na gasar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku