MATASHI YA YI YUNKURIN HALAKA KANSA DA KANSA A GARIN BAUCHI







Ke duniya ina zaki damu ne? wai wani dalili zai sanya mutum da hankalinsa zai dauki gabaran kashe kansa da kansa, a irin wannan rayuwar da kowa ta kansa yake, kowa na son ya tsira da na bakinsa!

A nan, jaridar Rariya ta ruwaito labarin wani matashi da ya nemi ya hallaka kansa a jihar Bauchi, inda tace wannan matashi ya siyo guba, kuma ya zube shi kaf a cikin abincinsa, Indomie, ba tare da bata lokaci ba ya fara saka loma, tare da yana sane da abinda yake ci.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Railway dake cikin garin Bauchi, inda ta kara da cewa a yayin da wannan dan kasada ke cikin saka loma, sai ya yanke jiki ya fadi, ya fara shure shuren mutuwa.

Sai dai mutanen da lamarin ya faru a gabansu basu kyale shi ya cika burinsa ba, inda nan take suka laluba aljihunsa, suka samu wata tsohuwar naira dari biyu, anan suka gaggauta sayo masa madara, wanda suka zazzage masa ita a bakinsa. Amma fa har yanzu babu tabbacin halin da wannan bawan Allah ke ciki, kamar yadda majiyar tamu ta tabbatar, haka zalika babu wani musabbabin yin haka da aka ruwaito.



Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments