LAI MOHAMMED YA SABA UMURNI NA YAYIN DA MAYAR WA OBASANJO MARTANI - BUHARI
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya hana
mashawarcinsa na musamman kan kafafen yadda labarai Femi Adesina mayar da
martani ga wasikar tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo saboda ba sa'an
sa bane.
Shugaba Buhari ya yi wannan bayanin ne lokacin
da ya ke karbar bakuncin kungiyar magoya bayansa a fadar Aso Villa da ke Abuja
a daren jiya. Buhari ya kuma ce dalili na biyu da ya sa bai mayar da martani
kan wasikar ba shine saboda shi da Obasanjo dukkansu sojoji ne
Ya lura cewa Lai Mohammed ya fede wa 'yan
Najeriya biri har wutsiya a kan halin da tattalin arzkin Najeriya ke ciki yayin
da gwamnatinsa ta karbi mulki a shekarar 2015 da kuma kokarin da gwamnatin keyi
na kawo gyra. "Ya ce dole in bar shi ya mayar da martani; saboda na san
cewa shi kwararen dan jarida ne sai na saurare shi na tambayi abinda zai fada.
"Sai ya ce zai tunatar da yan Najeriya halin da muka tsinci kan lokacin da
muka karba mulki a shekarar 2015 da halin da muke ciki a yanzu da kuma abubuwan
da muka aikata da kudaden da ke hannun mu. "Na kuma fahimci cewa ya yi
aiki mai kyau saboda mutane da dama sun kira ni a way suna shaida min cewa Lai
Mohammed ya mayar da martani yadda ya dace." Shugaban kasan ya mika
godiyarsa ga tawagar magoya bayansa bisa ziyarar da suka kawo masa musamman a
irin wannan wata mai albarka tare da yabon da suka yi masa game da nasarorin da
ya samu.
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku