KOTU TAKI BAYAR DA BELIN TSOHON GWAMNAN TARABA
Wata babbar kotun tarayya ta soke bukatar da tsohon gwamnan jihar Taraba Reverend Jolly Nyame, ya kai na neman a bada belin shi
An yanke wa Nyame hukuncin shekaru 14 a gidan maza sakamakon
kama shi da aka yi dumu - dumu da laifin cin hanci da rashawa, ya tunkari kotun
da bukatar beli saboda rashin lafiyar shi. Amma, mai shari'a Adebukola Banjoko
ta soke bukatar tashi. Mai shari'ar tace babu wata shaida da Nyame ya nuna, na
cewa hukumar gidan yarin basu da kayan aikin da zasu kula da rashin lafiyar
shi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku