KOFIN DUNIYA: JAMI'AN TSARO SUNYI GARGAƊI AYI HATTARA DA HARIN ƳAN TA'ADDA A GIDAJEN KALLON KWALLO
- To fa masu zuwa gidan kallon kwallo sai ai hattara
- Domin hukumomin tsaro sunyi gargadin faruwar wani abu maras
dadi
- Sun yi gargadin cewa watakila 'yan ta'adda ka iya amfanin
da yanayin wajen kai hari
Hukumomi a Najeriya sun gargadi mutane da su zauna cikin
shiri da kuma sa ido a yayin da suke kallon wasan kwallon kafar gasar cin kofin
duniya, saboda akwai yiwuwar samun hare-hare a lokutan kallon wasanni.
Hukumar 'yan sanda tare da hukumar shige da fice ta kasa sun
bayyana haka ne a ranar 25 ga watan Yulin da muke ciki, inda suka ce yan tada
kayar baya suna nan suna kokarin ganin sun sake kawo farmaki wanda zai jefa
jama'a cikin rudani, musamman a guraren da suke da cinkoson mutane domin kallon
wasannin gasar cin kofin duniya. Hukumar tsaro ta kasa ta bada umarni ga
dukkanin wani shugaban yan sanda na kowace jiha da su kasance cikin shiri tare
da tsaurara tsaro, sannan suke bada rahoton yanayin da kowace jiha take ciki
lokaci zuwa lokaci.
Hukumar ta kara kira ga jami'an tsaro cewa ya kamata dukkan
wani kayan tsaro su kasance cikin shiri domin komai zai iya faruwa, kuma tsaron
dukiya da rayuwar al'umma ita ce abinda suka sa gaba. Ya zuwa yanzu dai a iya
cewa babu wata alama da aka gani game kallon wasanni da ake yi a gidajen kallo,
kuma babu wani bayani da aka samu game da hakan, sai dai idan ba a manta ba a
baya an samu gurare da dama wanda aka samu tashin boma-bomai.
A garin Damaturu a lokacin da ake wasan gasar cin kofin
duniya a kasar Brazil a shekarar 2014, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Yuli
2014 tsakanin kasar Brazil da kasar Mexico inda bam ya tashi har mutane 21 suka
rasa rayukansu sannan mutane 27 suka raunta. Har wa yau, a shekara ta 2012 an
samu inda wani bam ya tashi a gidan kallon kwallo a garin Jos dake jihar
Plateau wanda shima mutane da dama suka raunata. Najeriya dai ta tsinci kanta
wajen yaki da yan tada kayar baya na Boko Haram tun shekara ta 2009 wanda hakan
ya jawo salwantar rayukan mutane sama dubu goma (10,000) a yanki Arewa maso
gabas kawai.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku