KIRISTOCI SUNYI ZANGA-ZANGA A JOS
Kiristoci da dama sunyi zanga-zanga a babban birnin Jihar
Filato, Jos saboda nuna bacin ransu game da kashe-kashen da aka yi a wasu
sassan jihar a ranar Lahadi da ta gabata. Masu zanga-zangan sun mamaye titunan
birnin Jos sanye da bakaken tufafi da kwalaye dauke da rubutu daban-daban masu
bayyana irin abubuwan da ke damunsa a jihar tare da kira ga hukuma ta dauki
mataki. Rahottani da ya fito daga shugabanin yankunan da lamarin ya afku sun
bayyana cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200 amma hukumar
yan sanda ta ce mutane 86 ne suka rasu.
A dai yau ne Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da
shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki suka garzaya jihar ta Filato don yin
jaje ga al'ummar jihar bisa rashin da su kayi.
Shima shugaba Buhari ya ziyarci jihar ta Filato a jiya Talata
26 ga watan Yuni inda ya bayyana al'ummar jihar cewa gwamnatinsa tana iya
kokarinta na ganin ta kare rayyuka da dukiyoyin al'umma a duk sassan kasar nan.
A bangarensa, gwamna Lalong na Jihar Filato ya ce wasu marasa ganin an
zauna lafiya ne suka kai harin a jihar, ya kuma shaida wa mutanen jihar cewa
gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an binciko wanda ke da hannu cikin harin don
su fuskanci hukunci.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku