KA HUKUNTA MASU A HANNU A KASHE - KASHEN JIHAR FILATO - SAKON GWAMNONI GA SHUGABA BUHARI



Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar fito da wadanda suke da hannu a kashe - kashen da ake yi jihar Filato kuma ya dauki kwakkwaran mataki akan su wurin gabatar hukunci akan su
A zaman da gwamnonin jihohin Najeriya suka yi a Abuja jiya, gwamnonin sun bukaci yin taro da manyan manyan kasar nan domin kawo karshen kashe - kashen da ake yi a jihar. Shugaban kungiyar gwamnonin na Najeriya, Abdulaziz Yari, wanda yayi magana da manema labarai jim kadan bayan sun tashi daga taron, gwamnan yace sun tattauna akan abubuwa da dama da suke addabar kasar nan musamman ma kashe - kashen da ake yi a jihar Filato. Bayan haka kuma gwamnonin sun nuna godiyar su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo da irin kokarin da suke nunawa domin ganin an kawo karshen rikicin a jihar. Sannan sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi iya bakin kokarin sa wurin hukunta duk wanda aka kama da laifi a kashe - kashen da yake faruwa a jihar.


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments